ABNA24 : Rahotanni sun ce shugabannin ƙasashen Afirka guda biyar ne da suka haɗa da na Botswana, Malawi, Afirka ta kudu da kuma Zimbabwe ne suka gana shugaban ƙasar Mozambique ɗin Filipe Nyusi a birnin na Maputo a jiya Alhamis don tattaunawa kan matsala tsaro da ayyukan masu ikirarin jihadi a arewacin ƙasar.
A ƙarshen taron na su dai, shugabannin sun fitar da wata sanarwa ta bayan taro da ta ce ƙasashen sun ƙuduri aniyar cewa ba za a su bari irin wannan lamari mai tada hankali da ke faruwa a Mozambique ya ci gaba da faruwa ba, sai dai ba su yi ƙarin bayani kan matakan da za su ɗauka wajen cimma wannan manufa da suka sa a gaba.
Kafin tattaunawar dai shugaban Mozambique ɗin, Filipe Nyusi ya ce gwamnatinsa tana dubi cikin yanayin neman taimakon ƙasashen waje.
Sama da mutane 2600 ne dai aka kashe, kana wasu 670,000 suka gudu suka bar muhallinsu sakamakon rikicin da ya fara ɓarkewa a ƙasar a shekara ta 2017, na baya-bayan nan shi ne wanda masu ikirarin jihadi waɗanda kuma suke da alaƙa da ƙungiyar ta’addancin nan ta Daesh (ISIS) suka kama wasu yankuna na ƙasar don abin da suka kira kafa gwamnatin halifanci.
342/